1. Da Yowab ɗan Zeruya, ya gane zuciyar sarki ta koma kan Absalom,
2. sai ya aika zuwa Tekowa a kira masa wata mace mai hikima. Da ta zo, ya ce mata, “Ki yi kamar kina makoki, ki sa rigunan makoki, kada ki shafa mai. Ki yi kamar wadda ta yi kwanaki da yawa tana makokin rasuwar wani.
3. Sa'an nan ki tafi wurin sarki, ki ce masa haka.” Sai ya faɗa mata abin da za ta faɗa.
4. Sa'ad da macen nan da ta zo daga Tekowa ta isa gaban sarki, sai ta rusuna har ƙasa don bangirma. Sa'an nan ta ce, “Ya sarki, ka yi taimako.”
5. Sai sarki ya tambaye ta, “Me ya dame ki?”Ta ce, “Ni mace ce wadda mijinta ya rasu.
6. Baranyarka tana da 'ya'ya biyu maza, sai suka yi faɗa a gona, inda ba wanda zai raba su, ɗayan kuwa ya bugi ɗayan ya kashe shi.
7. Yanzu kuwa dukan dangi sun tasar mini, suna cewa, in ba da ɗayan wanda ya kashe ɗan'uwansa domin su kashe shi saboda ran ɗan'uwansa da ya kashe. Wato za su hallaka magāji ke nan, ta haka za a yi biyu babu ke nan, su bar mijina ba suna ko zuriya a duniya.”
8. Sarki kuwa ya ce mata, “Ki tafi gidanki, zan daidaita maganarki.”
9. Sai ta ce wa sarki, “Ya ubangijina, sarki, bari laifin ya zauna a kaina da gidan mahaifina, sarki kuwa da gadon sarautarsa ya barata.”
10. Sarki ya ce mata, “In wani ya ƙara ce miki wani abu, ki kawo shi wurina, ba zai ƙara yi miki fitina ba.”
11. Sai ta ce, “Ina roƙonka, ya sarki, ka rantse da Ubangiji Allahnka, kada a bar masu bin hakkin jini su yi ramako, don kada su kashe ɗana.”Ya ce mata, “Na rantse miki da zatin Ubangiji, ko gashin kansa guda ɗaya ba zai faɗi ƙasa ba.”