9. Ta juye wainar daga kaskon yana gani, amma ya ƙi ci. Ya ce wa waɗanda suke cikin ɗakin su fita. Su kuwa suka fita.
10. Sa'an nan Amnon ya ce wa Tamar, “Kawo abincin a cikin ɗakin kwanana, ki riƙe mini in ci.” Sai ta ɗauki wainar da ta yi, ta kai wa Amnon, wanta, a ɗakin kwana.
11. Amma da ta kawo kusa da shi don ya ci, ya kama ta, ya ce, “Zo in kwana da ke ƙanwata.”
12. Ta ce masa, “Haba, wana, kada ka ƙasƙantar da ni, gama ba a yin haka a cikin Isra'ila, kada ka yi halin dabba.
13. Ni kuwa ina zan sa kaina saboda kunya? Kai kuwa za ka zama ɗaya daga cikin riƙaƙƙun sakarkarin mutane na cikin Isra'ila. Ina roƙonka ka yi magana da sarki, gama ba zai hana ka ka aure ni ba.”