2 Sam 1:21-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. “Kada ruwan sama ko raɓa su zubo kan tuddan Gilbowa.Da ma gonakinta su zama marasa ba da amfani.Gama a can ne aka zube garkuwoyin jarumawa a wulakance,Tsatsa ta rufe garkuwar Saul.

22. Bakan Jonatan mai kisa ne,Takobin Saul ba shi da jinƙai,Yana kashe masu iko, yana kuma kashe abokan gāba.

23. “Saul da Jonatan ƙaunatattu ne, suna da bansha'awa,A raye suna tare, haka kuma a mace suna tare.Sun fi gaggafa sauri,Sun fi zaki ƙarfi.

24. “Ku 'yan matan Isra'ila, ku yi makoki domin Saul!Ya suturta ku da mulufi mai ƙayatarwa,Ya yi muku adon lu'ulu'u da zinariya.

2 Sam 1