2 Kor 5:15-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Ya kuwa mutu ne saboda dukan mutane, domin waɗanda suke a raye, kada su yi zaman ganin dama a nan gaba, sai dai su yi zaman wannan da ya mutu saboda su, aka kuma tashe shi saboda su.

16. Saboda haka, a nan gaba ba mā ƙara duban kowane mutum bisa ga ɗabi'ar jiki kawai, domin ko da yake mun taɓa duban Almasihu bisa ga ɗabi'ar jiki, yanzu ba ma ƙara dubansa haka.

17. Saboda haka, duk wanda yake na Almasihu sabuwar halitta ne, tsohon al'amari duk ya shuɗe, ga shi, kome ya zama sabo.

2 Kor 5