2 Kor 2:9-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Na rubuto muku wannan takanas, domin in jarraba ku, in ga ko kuna yin biyayya ta kowace hanya.

10. Wanda kuka yafe wa kome, ni ma na yafe masa. Abin da na yafe kuwa, in dai har ma akwai abin yafewa, saboda ku ne na yafe masa, albarkacin Almasihu,

11. don kada Shaiɗan ya ribace mu, gama mu ba jahilan makidodinsa ba ne.

12. To, sa'ad da na zo Taruwasa in yi bisharar Almasihu, ko da yake an buɗe mini hanya a cikin Ubangiji,

13. duk da haka dai hankalina bai kwanta ba, domin ban tarar da ɗan'uwana Titus a can ba, saboda haka, sai na yi bankwana da su, na zarce na tafi Makidoniya.

14. Amma godiya ta tabbata ga Allah, shi da kullum yake yi mana jagaba mu ci nasara, albarkacin Almasihu, ta wurinmu kuma yake baza ƙanshin nan, na sanin Almasihu a ko'ina.

15. Don kuwa, a gun Allah mu ne ƙanshin Almasihu a cikin waɗanda ake ceto, da waɗanda suke a hanyar hallaka.

16. Ga na ƙarshe ɗin, ƙanshin nan warin mutuwa ne, mai kaiwa ga hallaka, ga na farkon kuwa, ƙanshin rai ne mai kaiwa ga rai. To, wa zai iya ɗaukar nauyin waɗannan abubuwa?

2 Kor 2