1 Tim 3:7-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Banda haka kuma, lalle ne yă zama mai mutunci ga waɗanda ba su a cikinmu, don kada yă zama abin zargi, yă faɗa a cikin tarkon Iblis.

8. Haka kuma masu hidimar ikkilisiya, lalle ne su zama natsattsu, ba masu baki biyu ba, ko mashaya, ko masu kwaɗayin ƙazamar riba.

9. Lalle ne su riƙi asirin bangaskiya da lamiri mai tsabta.

10. Sai an gwada su tukuna, in kuma an tabbata ba su da wani abin zargi, to, sai su kama aikin hidimar.

11. Haka kuma matan, lalle su zama natsattsu, ba masu yanke ba, amma masu kamunkai, masu aminci ta kowace hanya.

12. Masu hidima kuma su zama masu mata ɗaya ɗaya, masu sarrafa 'ya'yansu da sauran iyalinsu da kyau.

1 Tim 3