1 Tar 9:32-43 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4-6. Iyalin Yahuza guda ɗari shida da tasa'in suka zauna a Urushalima, shugabansu kuwa shi ne Utai ɗan Ammihud, jīkan Omri daga wajen Feresa. Waɗansu kakanninsu kuwa su ne Imri da Bani. Zuriyar Shela ɗan Yahuza suna da shugaba mai suna Asaya. Zuriyar Zera ɗan Yahuza kuwa, shugabansu Yuwel.

32. Waɗansu 'yan'uwansu Kohatawa suke lura da gurasar ajiyewa. Sukan shirya ta kowace Asabar.

33. Waɗannan su ne mawaƙa, da shugabannin gidajen kakannin Lawiyawa, waɗanda suka zauna a ɗakunan Haikali, ba su yin wani aiki dabam, gama dare da rana suke yin aikinsu.

34. Waɗannan su ne manyan shugabannin gidajen kakannin Lawiyawa a zamaninsu, wato waɗanda suka zauna a Urushalima.

35. Yehiyel ne ya kafa Gibeyon ya zauna a ciki, sunan matarsa Ma'aka,

36. ɗan farinsa kuma shi ne Abdon. Sa'an nan ga Zur, da Kish, da Ba'al, da Ner, da Nadab,

37. da Gedor, da Ahiyo, da Zakariya, da Miklot,

38. mahaifin Shimeya. Zuriyarsu ne suka zauna a Urushalima daura da 'yan'uwansu.

39. Ner ya haifi Kish, Kish kuma ya haifi Saul, Saul ya haifi Jonatan, da Malkishuwa, da Yishwi, da Ish-boshet.

40. Jonatan ya haifi Mefiboshet, Mefiboshet ya haifi Mika.

41. 'Ya'yan Mika, maza, su ne Fiton, da Melek, da Tareya, da Ahaz.

42. Ahaz ya haifi Yehowadda, Yehowadda ya haifi Allemet, da Azmawet, da Zimri. Zimri ya haifi Moza,

43. Moza ya haifi Bineya, da Refaya, da Eleyasa, da Azel.

1 Tar 9