4-6. Iyalin Yahuza guda ɗari shida da tasa'in suka zauna a Urushalima, shugabansu kuwa shi ne Utai ɗan Ammihud, jīkan Omri daga wajen Feresa. Waɗansu kakanninsu kuwa su ne Imri da Bani. Zuriyar Shela ɗan Yahuza suna da shugaba mai suna Asaya. Zuriyar Zera ɗan Yahuza kuwa, shugabansu Yuwel.
29. Aka sa waɗansu su zama masu lura da kayayyakin Haikalin, da kayayyakin aiki na cikin Wuri Mai Tsarki, da lallausan gari, da ruwan inabi, da mai, da turare, da kayan yaji.
30. Waɗansu 'ya'yan firistoci, maza, suke harhaɗa kayan yaji.
31. Mattitiya, ɗaya daga cikin Lawiyawa, ɗan farin Shallum na iyalin Kora, shi ne mai lura da toya waina.
32. Waɗansu 'yan'uwansu Kohatawa suke lura da gurasar ajiyewa. Sukan shirya ta kowace Asabar.
33. Waɗannan su ne mawaƙa, da shugabannin gidajen kakannin Lawiyawa, waɗanda suka zauna a ɗakunan Haikali, ba su yin wani aiki dabam, gama dare da rana suke yin aikinsu.
34. Waɗannan su ne manyan shugabannin gidajen kakannin Lawiyawa a zamaninsu, wato waɗanda suka zauna a Urushalima.
35. Yehiyel ne ya kafa Gibeyon ya zauna a ciki, sunan matarsa Ma'aka,
36. ɗan farinsa kuma shi ne Abdon. Sa'an nan ga Zur, da Kish, da Ba'al, da Ner, da Nadab,
37. da Gedor, da Ahiyo, da Zakariya, da Miklot,
38. mahaifin Shimeya. Zuriyarsu ne suka zauna a Urushalima daura da 'yan'uwansu.
39. Ner ya haifi Kish, Kish kuma ya haifi Saul, Saul ya haifi Jonatan, da Malkishuwa, da Yishwi, da Ish-boshet.
40. Jonatan ya haifi Mefiboshet, Mefiboshet ya haifi Mika.