1 Tar 9:1-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Haka kuwa aka lasafta Isra'ilawa bisa ga asalinsu. An rubuta su a littafin sarakunan Isra'ila.Sai aka kai mutanen Yahuza zaman talala a Babila saboda rashin amincinsu ga Ubangiji.

2. Waɗanda suka fara zama a biranen mallakarsu, su ne Isra'ilawa da firistoci, da Lawiyawa, da kuma ma'aikatan Haikali.

3. Waɗansu mutanen Yahuza, da na Biliyaminu, da na Ifraimu, da na Manassa suka zauna a Urushalima.

7. Ga zuriyar Biliyaminu a Urushalima bi da bi, da Sallai ɗan Meshullam, da Hodawiya, da Hassenuwa,

8. da kuma Ibneya ɗan Yeroham, da Ila ɗan Uzzi, wato jīkan Mikri, da Meshullam ɗan Shefatiya, da Reyuwel, da Ibnija.

9. Tare da danginsu a zamaninsu, sun kai ɗari tara da hamsin da shida ne. Duk waɗannan shugabannin gidajen kakanninsu ne.

10. Daga cikin firistoci masu zama a Urushalima su ne Yedaiya, da Yehoyarib, da Yakin,

11. da Azariya ɗan Hilkiya, shi ne jami'in Haikalin Ubangiji, kakanninsa sun haɗu da Shallum ɗan Zadok, da Merayot, da Ahitub,

1 Tar 9