69. da Ayalon duk da makiyayarta, da Gatrimmon duk da makiyayarta.
70. Daga cikin rabin kabilar Manassa kuma an ba su Ta'anak duk da makiyayarta, da Bileyam duk da makiyayarta. An ba da waÉ—annan ga sauran iyalai na 'ya'yan Kohat, maza.
71. Daga na rabin kabilar Manassa na gabas, an ba 'ya'yan Gershon, maza, Golan ta Bashan tare da makiyayarta, da Ashtarot duk da makiyayarta.
72. Daga na kabilar Issaka kuma an ba su Kishiyon duk da makiyayarta, da Daberat duk da makiyayarta,
73. da Ramot duk da makiyayarta, da Enganin duk da makiyayarta.
74. Daga cikin kabilar Ashiru kuma an ba da Mishal duk da makiyayarta, da Abdon duk da makiyayarta,
75. da Helkat duk da makiyayarta, da Rehob duk da makiyayarta.