1 Tar 4:38-40 Littafi Mai Tsarki (HAU)

38. Waɗannan da aka jera sunayensu, su ne shugabannin iyalansu da gidajen kakanninsu.Sun ƙaru ƙwarai.

39. Suka yi tafiya har zuwa mashigin Gedor, zuwa gabashin kwarin don nemar wa garkunansu makiyaya.

40. A can suka sami makiyaya mai kyau mai dausayi. Ƙasar kuwa tana da faɗi, babu fitina, sai salama, gama mazaunan wurin a dā Hamawa ne.

1 Tar 4