15. 'Ya'yan Kalibu, maza, ɗan Yefunne, su ne Airu, da Ila, da Na'am. Ila shi ya haifi Kenaz.
16. 'Ya'yan Yehallelel, maza, su ne Zif, da Zifa, da Tiriya, da Asarel.
17-18. 'Ya'yan Ezra, maza, su ne Yeter, da Mered, da Efer, da Yalon. Bitiya 'yar Fir'auna, wadda Mered ya aura, ta haifi waɗannan, Maryamu, da Shammai, da Ishaba wanda ya haifi Eshtemowa. Mered kuma ya auri wata daga kabilar Yahuza, ta haifi Yered wanda ya kafa garin Gedor. Eber kuma ya kafa garin Soko, Yekutiyel kuwa ya kafa garin Zanowa.
19. 'Ya'ya maza na matar Hodiya 'yar'uwar Naham, su ne suka zama kakannin Kaila, Bagarme, da Eshtemowa da suke zaune a Ma'aka.
20. 'Ya'yan Shimon, maza, su ne Amnon, da Rinna, da Ben-hanan, da Tilon.'Ya'yan Ishi, maza kuwa, su ne Zohet da Ben-zohet.
21. 'Ya'yan Shela, maza, ɗan Yahuza, su ne Er wanda ya kafa garin Leka, da La'ada wanda ya kafa garin Maresha, da iyalan gidan masu aikin lilin da suke zaune a Bet-ashbeya,
22. da Yokim, da mutanen da suke zaune a Kozeba, da Yowash, da Saraf, waɗanda suka yi sarauta a Mowab, sa'an nan suka zauna a Baitalami. (Waɗannan labaru na tun dā ne.)