5. Waɗanda aka haifa masa a Urushalima, su ne Shimeya, da Shobab, da Natan, da Sulemanu, su huɗu ke nan waɗanda Bat-sheba 'yar Ammiyel ta haifa masa.
6. Yana da waɗansu 'ya'ya kuma, su ne Ibhar, da Elishuwa da Elifelet,
7. da Noga, da Nefeg, da Yafiya,
8. da Elishama, da Eliyada, da kuma Elifelet, su tara ke nan.
9. Waɗannan duka su ne 'ya'yan Dawuda, maza, banda 'ya'yan ƙwaraƙwarai. Tamar ita ce 'yar'uwarsu.
10. Waɗannan su ne zuriyar Sulemanu, daga Rehobowam, sai Abaija, da Asa, da Yehoshafat,
11. da Yoram, da Ahaziya, da Yowash,