22. Na wajen Izhara, shi ne Shelomit, na wajen Shelomit, shi ne Yahat.
23. Na wajen Hebron, su ne Yeriya na fari, da Amariya, da Yahaziyel, da Yekameyam.
24. Na wajen Uzziyel, shi ne Mika, na wajen Mika, shi ne Shamir.
25. Ɗan'uwan Mika, shi ne Isshiya. Na wajen Isshiya, shi ne Zakariya.
26. Na wajen Merari, Mali da Mushi, da Yayaziya. Na wajen Yayaziya, shi ne Beno.
27. Na wajen Merari, wato na wajen Yayaziya, su ne Beno, da Shoham, da Zakkur, da Ibri.
28. Na wajen Mali, shi ne Ele'azara wanda ba shi da 'ya'ya maza.
29. Na wajen Kish, ɗan Kish, shi ne Yerameyel.