Dawuda fa da shugabannin Lawiyawa suka zaɓi waɗansu daga cikin 'ya'yan Asaf, maza, da na Heman, da na Yedutun domin su raira waƙa da garayu, da molaye, da kuge. Ga waɗanda suka yi wannan hidima.