1 Tar 2:47-53 Littafi Mai Tsarki (HAU)

47. 'Ya'yan Yadai, maza, su ne Regem, da Yotam, da Geshan, da Felet, da Efa, da Sha'af.

48. Ma'aka, ƙwarƙwarar Kalibu, ta haifi Sheber da Tirhana.

49. Ta kuma haifi Sha'af mahaifin Madmanna, da Shewa mahaifin Makbena, da mahaifin Gibeya.'Yar Kalibu ita ce Aksa.

50. Waɗannan su ne zuriyar Kalibu, maza.'Ya'yan Hur, maza, wato ɗan farin Efrata, su ne Shobal wanda ya kafa Kiriyat-yeyarim,

51. da Salma, shi kuwa ya kafa Baitalami, da Haref ɗansa kuma wanda ya kafa Bet-gader.

52. Shobal yana da waɗansu 'ya'ya maza, su ne Rewaiya da wanda yake kakan rabin Manahatiyawa,

53. da iyalan da suke a Kiriyat-yeyarim, da na Itiriyawa, da na Futiyawa, da na Shumatiyawa, da na Mishraiyawa. Daga waɗannan ne Zoratiyawa da Eshtawoliyawa suka fito.

1 Tar 2