20. Hur shi ne mahaifin Uri, Uri kuwa shi ne mahaifin Bezalel.
21. Bayan haka sai Hesruna ya shiga wurin 'yar Makir mahaifin Gileyad, wadda ya aura sa'ad da yake da shekara sittin da haihuwa. Ta haifa masa Segub.
22. Segub shi ne mahaifin Yayir wanda yake da birane ashirin da uku a ƙasar Gileyad.
23. Amma sai Geshur da Aram suka ƙwace garuruwan Hawwotyayir ɗin daga gare su, har da Kenat da ƙauyukanta, garuruwa sittin. Duk waɗannan su ne zuriyar Makir mahaifin Gileyad.
24. Bayan rasuwar Hesruna, Abaija, matarsa, ta haifa masa Ashur, mahaifin Tekowa.
25. 'Ya'yan Yerameyel ɗan farin Hesruna, su ne Arama ɗan fari, sa'an nan Buna, da Oren, da Ozem, da Ahaija.
26. Sai Yerameyel ya auro wata mace, sunanta Atara. Ita ce mahaifiyar Onam.
27. 'Ya'yan Arama, ɗan farin Yerameyel, su ne Ma'az, da Yamin, da Eker.
28. 'Ya'yan Onam, maza, su ne Shammai da Yada. 'Ya'yan Shammai, maza, su ne Nadab da Abishur.
29. Sunan matar Abishur Abihail, ta haifa masa Aban da Molid.
30. 'Ya'yan Nadab, maza, su ne Seled da Affayim, amma Seled ya rasu bai bar 'ya'ya ba.
31. Ɗan Affayim shi ne Ishi. Ɗan Ishi kuwa shi ne Sheshan. Ɗan Sheshan shi ne Alai.
32. 'Ya'yan Yada, maza, ɗan'uwan Shammai, su ne Yeter da Jonatan. Amma Yeter ya rasu bai bar 'ya'ya ba.
33. 'Ya'yan Jonatan su ne Felet da Zaza. Waɗannan su ne zuriyar Yerameyel.
34. Sheshan ba shi da 'ya'ya maza, sai dai 'ya'ya mata. Amma yana da wani bara Bamasare mai suna Yarha.
35. Sai Sheshan ya aurar wa Yarha baransa da 'yarsa, ita kuwa ta haifar masa Attai.