4. Hanun kuwa ya kama fādawan Dawuda, ya aske gyammansu, ya yanyanke rigunansu a tsaka daga wajen kwankwaso, sa'an nan ya sallame su.
5. Waɗansu mutane kuwa suka je suka faɗa wa Dawuda abin da ya sami mutanen. Sai ya aiko a tarye su, gama an ƙasƙanta mutanen nan da gaske. Sai sarki ya ce, “Ku zauna a Yariko, har lokacin da gyammanku suka tohu sa'an nan ku iso.”
6. Sa'ad da Ammonawa suka ga sun mai da kansu abin ƙi ga Dawuda, sai Hanun da Ammonawa suka aika da talanti dubu (1,000) na azurfa don su yi ijara da karusai da mahayan dawakai daga Mesofotamiya, da jihohin Ma'aka ta Suriya, da Zoba.
7. Suka yi ijarar karusai dubu talatin da dubu biyu (32,000), da Sarkin Ma'aka, tare da jama'arsa. Suka zo suka kafa sansani a gaban Medeba. Ammonawa kuwa suka tattaru daga biranensu don su yi yaƙi.
8. Da Dawuda ya ji labari, sai ya aiki Yowab tare da dukan sojoji, ƙarfafan mutane.
9. Sai Ammonawa suka fito suka jā dāga a ƙofar birninsu. Sarakunan da suka zo suka ware suka zauna a saura.