1 Tar 14:16-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Dawuda fa ya yi daidai yadda Ubangiji ya umarce shi. Suka bugi sojojin Filistiyawa tun daga Geba har zuwa Gezer.

17. Sunan Dawuda kuma ya kai ko'ina cikin dukan ƙasashe. Ubangiji kuwa ya sa dukan al'ummai su ji tsoron Dawuda.

1 Tar 14