3. Sa'an nan mu ɗauko akwatin alkawari na Allahnmu mu kawo shi wurinmu, gama mun ƙyale shi tun zamanin Saul.”
4. Jama'a kuwa suka amince da shawarar, suka yarda kuma a yi haka ɗin.
5. Haka fa, Dawuda ya tattara dukan Isra'ilawa wuri ɗaya, daga Shihor ta Masar, har zuwa mashigin Hamat domin a kawo akwatin alkawari na Allah daga Kiriyat-yeyarim.
6. Sai Dawuda tare da dukan Isra'ilawa, suka haura zuwa Ba'al, wato Kiriyat-yeyarim ta Yahuza, domin su ɗauko akwatin alkawarin Allah daga can, inda ake kira bisa sunan Ubangiji, wanda kuma yake zaune a wurin kerubobi.