1 Tar 12:40 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Waɗanda kuma suke kusa da su har zuwa Issaka, da Zabaluna da Naftali, sun kawo abinci a kan jakuna, da raƙuma, da alfadarai, da takarkarai. Suka kawo abinci mai yawa, wato gāri da kauɗar ɓaure da nonnan busassun 'ya'yan inabi, da ruwan inabi, da man zaitun. Suka kuma kawo shanu da tumaki domin yanka a ci. Duk an yi wannan domin a nuna farin ciki ƙwarai a cikin dukan ƙasar Isra'ila.

1 Tar 12

1 Tar 12:38-40