1 Tar 11:14-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Sai shi da Dawuda suka shiga gonar sha'ir ɗin, suka tsaya ciki don su tsare ta. Suka ragargaza Filistiyawa, Ubangiji kuwa ya cece su, ya ba su babbar nasara.

15. Wata rana sai uku daga cikin manyan mutanen nan talatin suka gangara zuwa dutsen Dawuda, a kogon Adullam, sa'ad da rundunar sojojin Filistiyawa suka kafa sansani a kwarin Refayawa.

16. Dawuda yana cikin kagara, sojojin Filistiyawa kuwa suna a Baitalami.

1 Tar 11