7. Sa'ad da dukan Isra'ilawa waɗanda suke zaune a kwari suka ga sojojin sun gudu, Saul kuma da 'ya'yansa maza sun mutu, sai suka bar garuruwansu suka gudu. Filistiyawa suka zo suka zauna a wurin.
8. Kashegari, sa'ad da Filistiyawa suka tafi su kwashe waɗanda aka kashe, sai suka tarar da Saul da 'ya'yansa maza matattu a Dutsen Gilbowa.
9. Suka kuwa tuɓe tufafinsa, suka datse kansa suka ɗauka duk da kayan yaƙinsa, suka aiki manzanni ko'ina a ƙasar Filistiyawa don su ba gumakansu da jama'arsu wannan albishir.
10. Sai suka ajiye kayan yaƙin Saul a gidan gumakansu, suka kuma rataye kansa a gidan gunkin nan, wato Dagon.