11. har firistoci ba su iya tsayawa su gama hidima ba saboda girgijen, gama ɗaukakar Ubangiji ta cika Haikalin Ubangiji.
12. Sa'an nan Sulemanu ya yi addu'a ya ce,“Ubangiji ya ce zai zauna cikingizagizai masu duhu.
13. Yanzu na gina maka ɗaki maidaraja,Wurin da za ka zauna har abada.”
14. Sa'an nan sarki Sulemanu ya juya, ya fuskanci jama'a suna tsaye, ya roƙi Allah ya sa musu albarka.
15. Ya ce, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allah na Isra'ila, wanda ya cika alkawarin da ya yi wa tsohona, Dawuda, da ya ce masa,
16. ‘Tun daga ran da na fito da mutanena Isra'ila, daga Masar, ban zaɓi wani birni daga cikin kabilan Isra'ila inda zan gina Haikali domin sunana ba, amma na zaɓi Dawuda ya shugabanci mutanena Isra'ilawa.’ ”
17. Sulemanu ya ci gaba, ya ce, “Tsohona, Dawuda ya yi niyyar gina wa Ubangiji Allah na Isra'ila ɗaki,
18. amma Ubangiji ya ce wa tsohona, Dawuda, ya ji daɗin niyyar da ya yi ta gina Haikali,
19. amma duk da haka ba zai gina Haikalin ba, sai ɗansa wanda za a haifa masa shi ne zai gina Haikali domin sunan Ubangiji.
20. Yanzu Ubangiji ya cika alkawarin da ya yi, gama na tashi a maimakon tsohona, Dawuda, na hau gadon sarautar Isra'ila, kamar yadda ya alkawarta, ga shi kuwa, na gina Haikali saboda Ubangiji Allah na Isra'ila.
21. A cikin Haikalin kuma na shirya wa akwatin alkawari wuri, inda alkawarin Ubangiji yake, wato alkawarin da ya yi wa kakanninmu sa'ad da ya fito da su daga ƙasar Masar.”
22. Sa'an nan Sulemanu ya tsaya a gaban bagaden Ubangiji a gaban dukan taron jama'ar Isra'ila. Ya ɗaga hannuwansa sama,