1 Sar 7:6-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Ya yi babban shirayi mai ginshiƙai, tsawonsa kamu hamsin, faɗinsa kamu talatin. Akwai kuma wani shirayi mai ginshiƙai a gabansa.

7. Ya kuma gina shirayi ta sarauta inda zai riƙa yin shari'a, ya rufe dukan daɓenta da itacen al'ul.

8. Ya gina gidan da zai zauna a farfajiya na ciki, wajen shirayi. ya kuma gina wa matarsa, 'yar Fir'auna, gida irin wannan.

9. Aikin gine-ginen nan, an yi shi da duwatsu masu tamani tun daga tushen har zuwa rufin. Sai da aka auna duwatsun sa'an nan aka yanka su da zarto, ciki da baya daidai da juna.

10. An kafa harsashin ginin da manyan duwatsu masu tsada, waɗansu kamu takwas waɗansu goma.

11. Daga sama kuma akwai duwatsu masu tsada waɗanda aka yanka su bisa ga ma'auni, da kuma itacen al'ul.

12. Babbar farfajiyar fāda, da filin Haikali na ciki da shirayin Haikalin yana da bangaye da jerin katakan al'ul domin kowane jeri uku na yankakkun duwatsu.

13. Sarki Sulemanu kuwa ya aika a kawo Huram daga Taya, gwanin aikin tagulla ne.

14. Shi ɗan wata mata ne daga kabilar Naftali wadda mijinta ya rasu. Huram mutumin Taya ne, maƙerin tagulla. Yana da hikima, da fahimi, da fasaha na iya yin kowane irin aiki da tagulla. Ya kuwa amsa kiran sarki Sulemanu, ya zo ya yi masa dukan aikinsa.

15. Ya kuwa yi ginshiƙi biyu na zubi da tagulla. Kowane ginshiƙi tsayinsa kamu goma sha takwas ne, da guru mai kamu goma sha biyu kewaye da shi.

16. Ya kuma yi dajiya biyu ta zubi da tagulla don a sa a kan ginshiƙan. Tsayin kowace dajiya kamu biyar ne.

1 Sar 7