8. Sarkin Isra'ila ya ce wa Yehoshafat, “Da sauran mutum ɗaya wanda za mu iya mu tambaya faɗar Ubangiji, shi ne Mikaiya ɗan Imla, amma ina ƙinsa, gama bai taɓa yin wani annabcin alheri a kaina ba, sai dai na masifa.”Yehoshafat ya ce, “Kada sarki ya faɗi haka.”
9. Sa'an nan Sarkin Isra'ila ya kirawo wani bafāde, ya ce masa, “Maza, ka taho da Mikaiya ɗan Imla.”
10. Sarkin Isra'ila da Yehoshafat, Sarkin Yahuza, suna zaune a kujerun sarautarsu, saye da tufafinsu a dandalin ƙofar Samariya. Annabawa kuwa suna annabci a gabansu.
11. Zadakiya ɗan Kena'ana ya yi ƙahonin ƙarfe, ya ce, “Ubangiji ya ce, ‘Da waɗannan ƙahoni za ka tunkuyi Suriyawa har su hallaka.’ ”
12. Dukan annabawan suka yi annabci iri ɗaya, suna cewa, “Ka haura zuwa Ramot, za ka yi nasara, gama Ubangiji zai ba da ita a hannunka.”