43. Ya bi halin tsohonsa, Asa, bai karkace ba. Ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji. Duk da haka ba a rushe wuraren tsafin na tuddai ba. Mutane suka yi ta miƙa hadayu, suka ƙona turare a tuddan.
44. Yehoshafat kuma ya ba Sarkin Isra'ila amana.
45. Sauran ayyukan Yehoshafat, da ƙarfin da ya nuna, da yadda ya yi yaƙi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza.
46. Ya kori dukan karuwai mata da maza da suka ragu a ƙasar a zamanin tsohonsa Asa.
47. A lokacin babu sarki a Edom sai wakili.
48. Yehoshafat ya yi jiragen ruwa a Tarshish don su tafi Ofir su kwaso zinariya, amma jiragen ba su tafi ba, gama jiragen sun farfashe a Eziyon-geber.
49. Sa'an nan Ahaziya, ɗan Ahab, ya ce wa Yehoshafat. “Ka bar barorina su tafi tare da naka a cikin jirage.” Amma Yehoshafat bai yarda ba.
50. Yehoshafat kuwa ya rasu, aka binne shi a inda aka binne kakanninsa a birnin kakansa Dawuda. Ɗansa Yehoram ya gaji sarautarsa.
51. Ahaziya, ɗan Ahab, ya ci sarautar Isra'ila a Samariya a shekara ta goma sha bakwai ta sarautar Yehoshafat, Sarkin Yahuza. Ya yi sarautar Isra'ila shekara biyu.
52. Ya yi zunubi a gaban Ubangiji. Ya bi halin tsohonsa da na tsohuwarsa, da na Yerobowam ɗan Nebat, wanda ya sa Isra'ila su yi zunubi.