1 Sar 12:1-2 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Rehobowam ya tafi Shekem, gama dukan mutanen Isra'ila sun tafi Shekem don su naɗa shi sarki.

2. Sa'ad da Yerobowam, ɗan Nebat, ya ji labari, gama a lokacin yana Masar inda ya gudu saboda sarki Sulemanu, sai ya komo daga Masar.

1 Sar 12