1 Sam 8:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Da Sama'ila ya tsufa, sai ya naɗa 'ya'yansa maza su zama alƙalan Isra'ila.

2. Sunan ɗansa na fari Yowel, na biyun kuma Abaija. Su ne alƙalai a cikin Biyer-sheba.

3. Amma 'ya'yansa ba su bi gurbin mahaifinsu ba, amma suka mai da hankalinsu ga neman kuɗi, suka yi ta cin hanci, suka danne gaskiya.

1 Sam 8