Suka yanke kansa, suka tuɓe makamansa. Suka aika manzannin a ƙasar Filistiyawa da suke kusa don su kai wannan albishir zuwa ga haikalin gumakansu, da mutanensu.