1 Sam 29:9-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Akish ya amsa wa Dawuda, ya ce, “A ganina kai marar laifi ne kamar mala'ikan Allah, duk da haka shugabannin sojojin Filistiyawa sun ce, ‘Ba zai tafi yaƙi tare da mu ba.’

10. Ka tashi da sassafe kai da barorin ubangijinka da suka zo tare da kai. Da gari ya waye sai ku kama hanya.”

11. Dawuda kuwa ya tashi da sassafe ya kama hanya tare da mutanensa zuwa ƙasar Filistiyawa, amma Filistiyawa suka haura zuwa Yezreyel.

1 Sam 29