19. Da Saul, da 'yan'uwanka, da dukan mazajen Isra'ila suna kwarin Ila, suna yaƙi da Filistiyawa.”
20. Kashegari sai Dawuda ya tashi tun da sassafe, ya bar tumaki a hannun wani makiyayi, ya ɗauki guzurin, ya tafi kamar yadda mahaifinsa, Yesse, ya umarce shi. Ya isa sansani daidai lokacin da runduna suke fita tana kirari na jān dāgar yaƙi.
21. Isra'ilawa da Filistiyawa suka jā dāga, runduna gāba da runduna.
22. Sai Dawuda ya bar abin da ya kawo a wurin mai jiran kaya, ya sheƙa zuwa bakin dāga domin ya gai da 'yan'uwansa.