1 Sam 1:11-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Ta yi wa'adi, ta ce, “Ya Ubangiji Mai Runduna, idan lalle ka dube ni, ni baiwarka, ka tuna da ni, ba ka manta da ni baiwarka ba, amma ka ba ni ɗa, ni ma sai in ba da shi ga Ubangiji dukan kwanakinsa, aska kuwa ba za ta taɓa kansa ba.”

12. Eli kuwa ya lura da bakin Hannatu sa'ad da take yin addu'a.

13. Gama ta yi addu'ar a zuci, ba a jin muryarta, sai dai leɓun motsi. Don haka Eli ya zaci tana maye ne,

14. ya kuwa ce mata, “Sai yaushe za ki daina maye? Ki daina shan ruwan inabi.”

15. Hannatu kuwa ta amsa ta ce, “Ba haka ba, ya shugabana, ni mace ce da take baƙin ciki ƙwarai. Ni ban sha ruwan inabi, ko wani abu mai sa maye ba, amma ina faɗa wa Ubangiji dukan abin da yake a zuciyata.

16. Kada ka zaci ni 'yar iska ce. Ni dai ina faɗar damuwata da tsokanar da ake yi mini ne.”

17. Sai Eli ya ce mata, “Ki sauka lafiya, Allah na Isra'ila ya amsa miki roƙonki.”

18. Ita kuma ta amsa, ta ce, “Bari baiwarka ta sami tagomashi a gare ka.” Sa'an nan ta tafi, ta ci abinci. Ba ta ƙara ɓata ranta ba.

19. Elkana da iyalinsa suka tashi tun da sassafe suka yi wa Ubangiji sujada, sa'an nan suka koma gidansu a Rama. Elkana fa ya kwana da matarsa, Hannatu. Ubangiji kuwa ya tuna da ita.

20. Ta yi juna biyu, ta haifa ɗa, ta raɗa masa suna Sama'ila, wato “Na roƙo shi daga wurin Ubangiji.”

21. Elkana da iyalinsa duka suka tafi Shilo domin su miƙa wa Ubangiji hadaya ta shekara shekara, ya kuma cika wa'adinsa.

1 Sam 1