1 Kor 7:5-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Kada ɗayanku yă ƙaurace wa ɗaya, sai ko da yardar juna zuwa wani ɗan lokaci kaza, don ku himmantu ga addu'a, sa'an nan ku sāke haɗuwa, kada Shaiɗan yă zuga ku ta wajen rashin kamewa.

6. Na fadi wannan ne bisa ga shawara, ba bisa ga umarni ba.

7. Da ma a ce kowa kamar ni yake mana! Sai dai kowa da irin baiwar da Allah ya yi masa, wani iri kaza, wani kuma iri kaza.

8. Abin da na gani ga waɗanda ba su yi aure ba, da kuma mata gwauraye, ya kyautu a gare su su zauna ba aure kamar yadda nake.

9. In kuwa ba za su iya kamewa ba, to, sai su yi aure. Ai, gwamma dai a yi aure da sha'awa ta ci rai.

10. Masu aure kuwa ina yi musu umarni, ba kuwa ni ba, Ubangiji ne, cewa kada mace ta rabu da mijinta

11. (in kuwa ta rabu da shi, sai ta zauna haka ba aure, ko kuwa ta sāke shiryawa da mijinta), miji kuma kada ya saki matarsa.

12. Ga sauran, ni nake faɗa, ba Ubangiji ba, in wani ɗan'uwa yana da mace marar ba da gaskiya, ta kuma yarda su zauna tare, to, kada yă rabu da ita.

13. Mace kuma mai miji marar ba da gaskiya, ya kuwa yarda su zauna tare, to, kada ta rabu da shi.

14. Don miji marar ba da gaskiya, a tsarkake yake a wajen matarsa. Mace marar ba da gaskiya kuma, a tsarkake take a wajen mijinta. In ba haka ba, zai zamana 'ya'yanku ba masu tsarki ba ne, amma ga hakika masu tsarki ne.

15. In kuwa shi, ko ita, marar ba da gaskiya ɗin yana son rabuwa, to, sai su rabu. A wannan hali, ɗan'uwa ko 'yar'uwa mai bi, ba tilas a kansu, domin Allah ya kira mu ga zaman lafiya.

16. Ke mace, ina kika sani ko za ki ceci mijinki? Kai miji, ina ka sani ko za ka ceci matarka?

17. Sai dai kowa yă yi zaman da Ubangiji ya sa masa, wanda kuma Allah ya kira shi a kai. Haka nake umarni a dukan Ikilisiyoyi.

18. Duk wanda Allah ya kira, wanda dā ma yake da kaciya, to, kada yă nemi zama marar kaciya. Wanda kuwa ya kira yana marar kaciya, to, kada yă nema a yi masa kaciya.

19. Don kaciya da rashin kaciya ba sa hassala kome, sai dai kiyaye umarnin Allah.

1 Kor 7