1 Kor 4:9-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Don a ganina, Allah ya bayyana mu, mu manzanni, koma bayan duka ne, kamar waɗanda mutuwa yake jewa a kansu, don mun zama abin nuni ga duniya, da mala'iku duk da mutane.

10. An ɗauke mu marasa azanci saboda Almasihu, wato, ku kuwa masu azanci cikin Almasihu! Wato, mu raunana ne, ku kuwa ƙarfafa! Ku kam, ana ganinku da martaba, mu kuwa a wulakance!

11. Har a yanzu haka, yunwa muke ji, da ƙishirwa, muna huntanci, ana bugunmu, kuma yawo muke yi haka, ba mu da gida.

12. Guminmu muke ci. In an zage mu, mukan sa albarka. In an tsananta mana, mukan daure.

13. In an ci mutuncinmu, mukan ba da haƙuri. Mun zama, har a yanzu ma, mu ne kamar jujin duniya, abin ƙyamar kowa.

14. Ba don in kunyata ku na rubuta wannan ba, sai dai don in gargaɗe ku a kan cewa, ku 'ya'yana ne, ƙaunatattu.

15. Ko da kuna da malamai masu ɗumbun yawa, amma ba ku da ubanni da yawa, don ni ne ubanku a cikin Almasihu ta wurin bishara.

1 Kor 4