1 Kor 3:15-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. In kuwa aikin wani ya ƙone, to, sai yă yi hasara, ko da yake shi da kansa zai tsira, amma kamar ya bi ta wuta ne.

16. Ashe, ba ku sani ku Haikalin Allah ne ba, Ruhun Allah kuma yana zaune a zuciyarku?

17. In wani ya ɓāta Haikalin Allah, Allah zai ɓāta shi. Gama Haikalin Allah tsattsarka ne, ku kanku Haikalinsa ne.

18. Kada kowa yă ruɗi kansa. In waninku ya zaci shi mai hikima ne, yadda duniya ta ɗauki hikima, sai yă mai da kansa marar hikima, domin ya sami zama mai hikima.

1 Kor 3