1 Kor 15:29-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

29. In ba haka ba, mene ne nufin waɗanda ake yi wa baftisma saboda matattu? In ba a ta da matattu sam, don me ake yi wa waɗansu baftisma saboda su?

30. Don me kuma nake a cikin hatsari a kowane lokaci?

31. Na hakikance 'yan'uwa, saboda taƙama da ku da nake yi a cikin Almasihu Yesu Ubangijinmu, a kowace rana sai na sallama raina ga mutuwa!

1 Kor 15