25. asiran zuciyarsa kuma su tonu. Ta haka sai ya fāɗi ya yi wa Allah sujada, yana cewa lalle Allah na cikinku.
26. To, ƙaƙa abin yake ne, 'yan'uwa? Duk sa'ad da kuka taru, wani yakan yi waƙar yabon Allah, wani kuma koyar da Maganar Allah, wani bayani, wani yin magana da wani harshe, wani kuma fassara. Sai dai a yi kome don ingantawa.
27. In kuwa waɗansu za su yi magana da wani harshe, kada su fi mutum biyu, matuƙa uku, su ma kuwa bi da bi, wani kuma yă yi fassara.
28. In kuwa ba mai fassara, sai kowannensu yă yi shiru a cikin taron Ikkilisiya, yă yi wa Allah magana a zuci.
29. Masu yin annabci kuma, sai dai biyu ko uku su yi magana, saura kuwa su auna maganar.
30. In kuwa an yi wa wani wanda yake zaune wani bayani, sai na farkon nan mai magana yă yi shiru.
31. Dukanku kuna iya yin annabci da ɗaya ɗaya, har kowa yă koya, yă koma sami ƙarfafawa.
32. Annabawa suna sarrafa ruhohinsu na annabci,