1. To, ina so ku sani, 'yan'uwa, dukan kakanninmu an kāre su ne a ƙarƙashin gajimare, dukansu kuma sun ratsa ta cikin bahar.
2. Dukansu kuwa an yi musu baftisma ga bin Musa a cikin gajimaren, da kuma bahar ɗin.
3. Duka kuwa sun ci abincin nan na ruhu,
4. duk kuma sun sha ruwan nan na ruhu. Domin sun sha ruwa daga Dutsen nan na ruhu, wanda ya yi tafiya tare da su. Dutsen nan kuwa Almasihu ne.
5. Duk da haka Allah bai yi murna da yawancinsu ba, har aka karkashe su a jeji.
6. To, ai, waɗannan abubuwa gargaɗi ne a gare mu, kada mu yi marmarin mugayen abubuwa, kamar yadda suka yi.
7. Kada fa ku zama matsafa kamar yadda waɗansunsu suke. A rubuce yake cewa, “Jama'a sun zauna garin ci da sha, suka kuma tashi suka yi ta rawa.”
8. Kada fa mu yi fasikanci yadda waɗansunsu suka yi, har mutum dubu ashirin da uku suka zuba a rana ɗaya tak.
9. Kada kuma mu gwada Ubangiji yadda waɗansu suka yi, har macizai suka hallaka su.