1 Kor 1:19-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. Domin a rubuce yake cewa,“Zan rushe hikimar mai hikima,Zan kuma shafe haziƙancin haziƙi.”

20. To, ina masu hikima suke? Ina kuma masana? Ina masu muhawwarar zamanin nan? Ashe, Allah bai fallashi hikimar duniyar nan a kan wauta ce ba?

21. Da yake bisa ga hikimar Allah, duniya ba ta san Allah ta wurin hikimarta ba, sai Allah ya ji daɗin ceton masu ba da gaskiya, ta wurin wautar shelar bishara.

22. Yahudawa kam, mu'ujiza suke nema su gani, Helenawa kuwa hikima suka nema su samu,

23. mu kuwa muna wa'azin Almasihu gicciyeyye, abin sa yin tuntuɓe ga Yahudawa, wauta kuma ga al'ummai,

24. amma ga waɗanda suke kirayayyu, ko Yahudawa ko al'ummai duka biyu, Almasihu ikon Allah ne, da hikimar Allah.

25. Domin abin da aka zata wauta ce ta Allah, ya fi hikimar ɗan adam, abin da kuma aka zata rauni ne na Allah, ya fi duk ƙarfin ɗan adam.

26. Ku dubi kiranku da aka yi, ya ku 'yan'uwa, a cikinku, ai, ba a kira masu hikima irin ta duniya da yawa ba, masu iko kuma ba su da yawa, haka ma masu asali ma ba yawa.

27. Amma Allah ya zaɓi abin da yake wauta a duniya, domin ya kunyata masu hikima. Allah ya zaɓi abin da yake rarrauna a duniya, domin ya kunyata ƙaƙƙarfa.

28. Allah ya zaɓi abin da yake ƙasƙantacce, wulakantacce a duniya, har ma abubuwan da ba su, domin yă shafe abubuwan da suke akwai.

29. Wannan kuwa duk don kada wani ɗan adam yă yi fariya a gaban Allah ne.

30. Gama Allah ne ya sa kuka zama na Almasihu Yesu, Allah ne kuma ya sa Almasihu ya zama hikima a gare mu. Ta wurin Almasihu ne kuma muka sami adalci, da tsarkakewa da fansa.

31. Saboda haka, “Duk mai yin alfarma, yă yi da Ubangiji” (abin da yake a rubuce ke nan).

1 Kor 1