5. Gama zan zama mata garu na wuta kewaye da ita, zan zama daraja a tsakiyarta, in ji Ubangiji.”
6. Ubangiji ya ce, “Yanzu ku gudu daga ƙasar arewa, gama na warwatsa ku a waje kamar iska ta kusurwoyi huɗu na duniya!
7. Ya ke Sihiyona, ku tsere, ku waɗanda kuke zaune a Babila.”
8. Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Bayan ɗaukaka ya aike ni zuwa wurin al'umman duniyan nan da suka washe ku, gama wanda ya taɓe ku, ya taɓi ƙwayar idona.
9. Ga shi, zan nuna ikona a kansu, za su kuwa zama abin waso ga waɗanda suka bauta musu. Sa'an nan za ku sani Ubangiji Mai Runduna ya aike ni.
10. “Ki raira waƙa, ki yi farin ciki, ya Sihiyona, gama ina zuwa, in zauna a tsakiyarki! Ni Ubangiji na faɗa.