10. “Ki raira waƙa, ki yi farin ciki, ya Sihiyona, gama ina zuwa, in zauna a tsakiyarki! Ni Ubangiji na faɗa.
11. “A wannan rana al'umman duniya da yawa za su haɗa kai da Ubangiji, za su kuwa zama jama'ata, ni kuma zan zauna a tsakiyarki. Za ki sani Ubangiji Mai Runduna ya aike ni gare ki.
12. Yahuza za ta zama abin mallakar Ubangiji a cikin tsattsarkar ƙasar. Zai kuma zaɓi Urushalima.”
13. Bari dukan 'yan adam su yi tsit a gaban Ubangiji, gama ya taso daga wurin zamansa mai tsarki.