Zab 90:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ya Ubangiji, a koyaushe kai ne wurin zamanmu.

2. Kafin a kafa tuddai,Kafin kuma ka sa duniya ta kasance,Kai Allah ne, Madawwami.Ba ka da farko, ba ka da ƙarshe.

3. Kakan sa mutane su koma yadda suke,Su zama ƙura.

4. A gare ka shekara dubu, kamar kwana ɗaya ne,Kamar jiya ce wadda ta shige,Gajeruwa ce kamar sa'a guda ta dare.

5. Kakan kwashe mutane kamar yadda ambaliyar ruwa take yi,Kamar mafarki suke, ba su daɗewa.Kamar tsire-tsire suke waɗanda suke tsirowa da safe,

6. Su yi girma har su yi huda,Sa'an nan su yi yaushi su bushe da yamma.

7. Mun halaka ta wurin fushinka,Mun razana saboda hasalarka.

8. Ka jera zunubanmu a gabanka,Zunubanmu na ɓoye kuwa,Ka sa su a inda za ka gan su.

9. Fushinka ya gajerta tsawon ranmu,Ranmu ya ƙare kamar ajiyar zuciya.

10. Tsawon kwanakin ranmu duka a ƙalla shekara ce saba'in,In kuwa muna da ƙarfi, shekara tamanin ne.Duk da haka iyakar abin da waɗannan shekaruSuke kawo mana, damuwa ce da wahala,Nan da nan sukan wuce,Tamu da ƙare.

Zab 90