Zab 76:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Allah sananne ne a Yahuza,Mashahuri ne kuma a Isra'ila.

2. Wurin zamansa yana Urushalima,A dutsen Sihiyona zatinsa yake.

3. A can yake kakkarya kiban abokan gāba,Da garkuwoyinsu, da takubansu, i, har da dukan makamansu.

4. Ina misalin darajarka, ya Allah!Ina misalin ɗaukakarka a sa'ad da ka komo daga kan duwatsu,Daga korar abokan gābanka!

5. An kwashe ganimar sojojinsu masu ƙarfin hali,Yanzu suna barci, barcin matattu,Ba waninsu da ya ragu,Da zai yi amfani da makamansa.

Zab 76