Zab 57:8-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Ka farka, ya raina!Ku farka, molona da garayata!Zan sa rana ta farka!

9. Zan gode maka a cikin sauran al'umma, ya Ubangiji!Zan yabe ka a cikin jama'a!

10. Madawwamiyar ƙaunarka ta kai har sammai,Amincinka kuma har sararin sammai.

11. Ka bayyana girmanka, ya Allah, a sararin sama,Ɗaukakarka kuma a bisa dukan duniya!

Zab 57