Zab 56:4-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Ga Allah nake dogara, ina yabon alkawarinsa,Gare shi na dogara, ba zan ji tsoro ba.Me mutum kawai zai yi mini?

5. Maƙiyana suke ta wahalshe ni dukan yini,A kan kowane abu da nake yi,Kullum suna ta tunanin yadda za su cuce ni!

6. Sukan taru a ɓoye,Suna kallon duk abin da nake yi.Suna sa zuciya za su iya kashe ni.

7. Ka hukunta su, ya Allah saboda muguntarsu,Da fushinka ka kori waɗannan mutane!

8. Ka san irin wahalar da nake sha,Kana riƙe da lissafin yawan hawayena.Ashe, ba a rubuce suke a littafinka ba?

9. A ranar da na yi kira gare ka,Za a komar da abokan gābana baya,Gama na sani Allah yana tare da ni!

Zab 56