Zab 42:5-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Me ya sa nake baƙin ciki haka?Me ya sa nake damuwa ƙwarai?Zan dogara ga Allah,Zan sāke yin yabonsa,Mai Cetona, Allahna.

6. Zuciyata ta karaiSaboda haka zan tuna da kaiA wajen Urdun, da kusa da Dutsen Harmon, da na Mizar,Zan tuna da kai.

7. Zurfafan tekuna suna kiran junansu,Matsirgar ruwa na Allah kuwa suna ta ruri!Igiyoyin ruwa na baƙin cikiSuka yi wa raina ambaliya.

8. Ubangiji ya nuna madawwamiyar ƙaunarsa kowace rana!Ni ma in raira yabo gare shi kowane dare,In yi addu'a ga Allah, wanda ya ba ni rai.

Zab 42