6. Ba ka bukatar baye-baye da hadayu,Ba ka so a miƙa maka hadayun ƙonawaNa dabbobi a bisa bagade ba,Ko baya-baye don a kawar da zunubai.A maimakon haka, ka ba ni kunnuwan da zan saurare ka.
7. Sai na amsa, “Ga ni, umarnanka zuwa gare niSuna a Littafin Shari'a.
8. Ina ƙaunar in aikata nufinka sosai, ya Allah!Ina riƙe da koyarwarka a zuciyata.”
9. A taron dukan jama'arka, ya Ubangiji,Na ba da albishir na cetonka.Ka sani ba zan fasa hurta shi ba.
10. Ban riƙe labarin cetonka don kaina kaɗai ba,Nakan yi maganar amincinka, da taimakonka a koyaushe.Ba na yin shiru a taron dukan jama'arka,Amma ina ta shaida madawwamiyar ƙaunarka da amincinka.