Zab 38:17-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Ina gab da fāɗuwa,Ina cikin azaba kullum.

18. Na hurta zunubaina,Sun cika ni da taraddadi.

19. Magabtana lafiyayyu ne masu ƙarfi.Waɗanda yake ƙina ba dalili, suna da yawa.

20. Masu rama nagarta da mugunta,Suna gāba da ni,Domin ina ƙoƙarin aikata abin da yake daidai.

21. Kada ka yashe ni, ya Ubangiji,Kada ka rabu da ni, ya Allahna!

22. Sai ka taimake ni yanzu, ya Ubangiji, Mai Cetona!

Zab 38