Zab 33:18-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Ubangiji yana kiyaye masu tsoronsa,Waɗanda suke dogara ga madawwamiyar ƙaunarsa.

19. Yakan cece su daga mutuwa,Yakan rayar da su a lokacin yunwa.

20. Ga Ubangiji muke sa zuciya,Shi mai taimakonmu ne, mai kiyaye mu.

21. Saboda da shi muke murna,Muna dogara ga sunansa mai tsarki.

Zab 33